Kira layin ‘yan sanda na Royal Oman a kan

800 77 444

Idan an kawo ku Oman ta hanyar alƙawarurrukan ƙarya, kuma yanayin aikinku ya sha bamban da yadda kuka zata, kuna iya zama waɗanda suka faɗa tarkon safarar mutane.

Shin ɗaya daga cikin waɗannan ya shafe ku?

  • An ɗauke fasfo ɗina.
  • Albashina ya yi ƙasa matuƙa da abin da aka yi mini alƙawari a kwangilata.
  • Ana tilasta ni in yi aiki fiye da sa’o’in da aka zayyana a cikin kwangilata ba tare da ƙarin albashi ba.
  • Ba a ba ni wata ranar hutun mako-mako ba kuma ba a biya na ladar aiki a ranakun hutuna.
  • Maigidana ya faɗa mini cewa yana bi na kuɗi sakamakon kawo ni da ya yi da kuma biyan bisana.
  • Maigidana ya yi ikirarin cewa yana bi na bashi saboda muhallin zama da magani ko abinci.
  • Wanda ya ɗauki nauyina ko hukumar da ta ɗauke ni tana bi na bashi sakamakon kawo ni cikin ƙasar.
  • Maigidana ya yi min barazanar za a kore ni idan na shigar da ƙara ga ’yan sanda ko Ma’aikatar Ƙwadago game da yanayin aikina
  • ‘Yan gidan da nake yi wa aiki suna cin zalina ko kuma suna taɓa ni yadda bai dace ba.
  • Maigidana yana duka na.
  • An yi min barazana mai ta da hankali.
  • Ana tilasta ni yin jima’i da maza.
  • Ina so na daina yin aikin karuwanci na koma gida amma shugabana ba zai ƙyale ni ba.

Idan haka ne, da alama kun kasance waɗanda ke cikin takunkumin safarar mutane.

Kuma ka tuna cewa kai wanda ke cikin takunkumi ne, ba mai laifi ba.

‘Yan sanda na Royal Oman a shirye suke su saurare ku. An horar da su don taimaka wa mutane irinku. Suna iya kare ku daga mai ba ku aiki. Za su iya kawo ƙarshen damuwarku.

Me zan yi?

Idan akan ba ku izinin fita waje da kanku, ku ziyarci matsugunin ‘yan sandan Royan Oman sannan ku sanar da su abin da ya faru da ku. Hakanan za ku iya buƙatar aboki ya tuntuɓe su a madadinku.

 Kira layin ‘yan sanda na Royal Oman a kan

800 77 444

Kira kyauta ne. Jami’an suna magana da Larabci da Ingilishi.

Idan ba za ku iya magana da Ingilishi ko Larabci ba, ku nemi wani da zai iya domin ya kira a madadinku.

Me zai faru bayan nan?

‘Yan sandan Royal Oman za su bincika lamarinku. Za su iya kai ku wani matsuguni na musamman don tabbatar da tsaronku da lafiyarku. Ma’aikatan tallafi za su tabbatar da cewa kuna cikin tsaro sannan za su samar muku da matsuguni da magani da sauran abubuwan da za ku buƙata a matsayinku na waɗanda ke cikin haɗari. Duk sabis kyauta ne ba tare da buƙatar sisi ba daga gare ku.